17 Disamba 2019 - 06:26
Shugaba Erdogan Ya gana Da Firaministan Kasar Libya

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya gana da Firaministan gwamnatin hadin kan kasar Libya Fayez al-Sarraj a Istanbul cikiyar kasuwancin kasar ta Turkiya , kwanaki bayan da shugaban yace a shirye yake ya tura dakaru zuwa Libya idan kasar ta bukaci haka.

(ABNA24.com) Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya gana da Firaministan gwamnatin hadin kan kasar Libya Fayez al-Sarraj a Istanbul cikiyar kasuwancin kasar ta Turkiya , kwanaki bayan da shugaban yace a shirye yake ya tura dakaru zuwa Libya idan kasar ta bukaci haka.

Babu dai cikkaken bayani kan ganawar da shugabannin biyu suka yi a asirce, amma a wata ganawa da suka yi ranar 27 ga watan Nuwamba, kasashen biyu sun amince da hada kai gami da aiki tare a bangare tsaro da kuma jiragen ruwa.

A bangare guda, ofishin jakadancin kasar Libiya dake birnin Alkahira ya sanar da rufe ofishin har zuwa wani lokaci saboda dalilai na tsaro a jiya Lahadi.

Kasashen Turkiya da Qatar na goyawa gwamnatin rikon kwaryar Libyar dake da hedkwata a birnin Tripoli baya, yayin da kasashen Saudi Arabia da Masar gami da Hadadiyar Daular Larabawa ke goyan bayan Khalifa Haftar dake kai hare-hare kan birnin Tripoli na nufin kwace shi daga gwamnatin hadin kan kasar da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita.


/129